Daraktan Labarai Na Sojojin Najeriya Yayi Murabus
Manjo Janar Cris Olukolade, Darekta labarai jami’an tsaro na shirin ritaya daga aikin sojan Najeriya.
Olukolade ya shiga shekarun ritaya. Kanar Rabe Abubakar zaya dauki wurinsa daga sati mai zuwa, Jaridar Punch ta ruwaito.
Wani ka kamfanin labarai ya bayyana sojojin Najeriya sun bayyana hakan a ranar Alhamis 30 ga watan Yuli.
Shugaban sojojin Najeriya, Manjo Janar Tukur Buratai ya amince da nada Abubakar a matsayin Darekta na labarai a ranar Laraba.
Kuma, Olukolade zaya hannanta shugabancin zauren masu magana da yawun jami’an tsaro ”Forum of Spokespersons of Security and Response Agencies (FOSSRA)’’ zuwa ga Commodore Kabiru Aliyu, shine Darektan labarai na sojojin ruwa a Najeriya.
Olukolade ya bayyana .a Abokai aikinsa a taron da FOSSRA akan ritayararsa lokacin ganawar da suka gudanar a ranar Alhamis 30 Yuli a Wurin na rage Cibiyar sadarwa ta rikici ‘’Centre for Crisis Communication (CCC)’’ a Abuja.
Olukolade ya amshi aikin Darekta na labarai daga Kanar Muhammad Yarima a Maris 2013. A lokacin shine Kwamanda na Makarantar labarai na Sojojin Najeriya a matsugunin Bonny, a Legas.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment